Yadda Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi) ya zama zara a cikin taurari
Yadda Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi) ya zama zara a cikin taurari
Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi)
Daga SANI AHMAD GIWA
Hausawa gwanayen hikimar iya sarrafa harshe, sun yi gaskiya da suke cewa, “Idan ana dara fitar da uwa ake yi,” shi ya sa har kullum, ake ci gaba da samun mutane da suka yi fice, suka yi zarra a fannonin inganta rayuwar jama’a ta yau da kullum. Sai dai kuma, ita wannan daukaka, ba haja ba ce, ko wata riga da za a baje a kasuwa domin kowa ya je, ya saya, ya saka, a’a, wannan baiwa ce ta min Indillahi, kyauta ce ta Ubangiji, wanda cikin hikimarsa ne yake fitar da amale a kowane garken rakuma.
Shakka babu a so shi ko a ki shi, a farfajiyar siyasar duniyar yau, siyasa a siyasance ya yi wa tsara ratar da sai dai su biyo baya, domin Allah ya tarfawa garinsa nono, kazalika zakaransa ya yi caran da aka jiwo amonsa a rukunin siyasar akida, siyasar ci gaban jama’a, bugu da kari siyasar gina al’umma.
A haka babban abin lura shi ne yana gudanar da siyasa ne a matakin sallama da salama, hasali ma ya yi hannun riga da siyasar gaba ko siyasar nunin yatsu, ballantana ya sa kansa a siyasar gaba da gaba, ko siyasar a mutu ko a yi rai, bare kuma irin siyasar nan ta yin amfani da matasa ta hanyar ba su qwayo suna sha suna aikata ta'asa. Duka wadannan ya yi hannun riga da su.
Wane ne wannan? Dakta Ibrahim Bello Dauda El-Daby, limamin kawo tsafta a siyasar Nijeriya, wanda a duniyar siyasar yau ba ya bukatar kowace irin gabatarwa idan ana maganar zarata kuma matasa ‘yan siyasar da suka himmatu, suka jajirce suka kuma yi tsayuwar dakan kyautata jin dadi da walwalar al’ummarsu ta yadda hidimta wa al'umma da yake yi ba tare da yana rike da wani mukamin zababben shugaba a Nijeriya ba tun fil azal, milyoyin al’umma ke ci gaba da morar dimbin alheransa da ya dasa a shekaranjiya da jiya, wanda yau ma ake cin moriyarsa.
Ko tababa babu ‘yan siyasa da masu fashin bakin lamuran siyasa sun yi ittafakin cewar matashin dan siyasar mai jini a jika, Dr. Ibrahim Bello Dauda dan siyasa ne, shugaba ne kuma jagoran jama’a, wanda fagen siyasar kasar nan ke tinkaho tare da alfahari da kasancewarsa a fagen, gwarzo ne da duniyar siyasarsa ta yi wa fagen siyasar kasar nan wankan tsarki, shi ya sa har kullum farin jininsa da karbuwarsa a wajen jama’a, ba su taba fuskantar nakasu ba, sabanin wasu takwarorinsa ‘yan siyasar bana-bakwai, wadanda tashin karbuwa da farin jininsu bai da bambanci da tashin gishirin andir.
Wanda Allah ne cikin ikonSa ya cusa tausayin al'ummar Nijeriya cikin zuciyar El-Daby kuma dabi'arsa ta gudanar da kyawawan ayyuka domin talakawa da marasa galihu su amfana da tarihin alkhairansa.
Ko da makaho ne wanda bai gani, sai a tambaye shi idan aka yi walkiya me ake gani? Amsar da zai bada ita ce haske! To tabbas Dr. El-Daby alamomi sun nuna cewa siyasar matashin kuma gogaggen masanin tattalin arziki mai tarin fasaha da fikira tare da dabarun gudanar da mulki, siyasar sa ta dauki haske, domin ko ba a fada ba har kullum dai ginin da zai yi karko da inganci, kana kuma ya yi tsawon kwana, ana dora shi ne akan tubali mai inganci, wanda zai iya jimirin nauyi da sauye-sauyen yanayi.
Haka lamarin yake a sauran al’amurran rayuwar jama’a, domin dukkanin wata tafiya ta jama’a, ana yi mata kyakkyawan shiri ne. Da irin wannan shirin ne wasu suka ga shekaranjiya, suka ga jiya, har ga shi yau ma ana damawa da su, kuma da rashin irin wannan shirin ne wasu suka yi ta-leko-ta-koma.
Da wannan, za a iya fahimtar cewa, a Nijeriya babu wata kujerar madafun mulki da Dr. Ibrahim Bello Dauda ba zai iya zaman kanta kuma ta dace da shi ba.
A tuna cewa, Dr. ya dade da fafe gorarsa, don ba zai sha ruwan sa da daci ba, domin kuwa ya san in da aka fito, ya san in da ake, don haka yana da yakinin in da alkiblar ya kamata ta dosa a gobe, domin ganin goben ta fi yau da jiya da ma shekaranjiya, sa’annan gata ko jibi, ta ginu akan kyakkyawan tafarkin da goben ta shimfida.
Ma’ana dai, ba hawan kawara matashin dattijon ya yi wa lamurran siyasa ba, kamar yadda wasu ke yi wa lamarin haye.
To sai dai kuma bai zamo dan koyo ba, domin ya karanci ciki da wajen tafiyar siyasa tun gabannin shigowa fagen, don haka ya san idan tafiyar ta karkace, ya san komadar da ke bukatar kwankwasar gudumar mutane irinsa, wannan ne ya taimaka masa wajen soma tafiyarsa da kafar dama.
Hausawa sun ce, Idan ka ji wane ba banza ba. A kan haka, kwarewa da gogewar da Dr. ya yo guzuri da ita daga fagen aikin gwamnati da kamfanoni in da ya shafe tsawon shekaru yana yi wa al’umma hidima, su suka haskaka masa hanyar daidaita lamurra, don haka da wannan guzuri na maganin zazzabin tafiyar siyasar kasar nan, El-Daby ya shigo fagen siyasa.
Dr. Ibrahim Bello Dauda ya shigo siyasa ne da aniyar sauya tunanin dubun dubatar wadanda ke yi wa shugabanci kallon wata kafa ta amfanar kai kurum, domin kuwa, a cikin manufofinsa da da yake amfani da su akwai akidar fifita muradun wadanda ake mulki a wajen aiwatar da duk wani abu da za ayi dominsu, wanda kuma zai amfanesu.
Wane ne Dr. Ibrahim Bello Dauda?
Matashin gogaggen dan siyasa a Nijeriya, kuma wanda ya yi sha'awar gadon kujerar Shugaba Buhari a 2023 a karkashin tutar Jam'iyyar APC, shine mafi karancin shekaru a APC cikin maza da suka nuna sha'awar gadon kujerar kafin zaven fidda gwanin da aka yi.
Dan Kabilar Kanuri ne a Jihar Borno. An haife shi 3 ga Yuni, 1972 a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.
Dr. El-Dabi ya taso a Jihar Filato inda ya yi mafi yawancin rayuwar shi da karatun shi a jihar. Ya fara karatun firamaren Mishan ta Roman Katolika da ke garin Girin a jihar ta Filato, daga nan ya wuce makarantar sakandiren sojoji da ke Zariya (Chindit Barrack).
Bayan ya kammala ya samu shiga makarantar School of Accountancy and Management Studies a garin na Jos, sai kuma makarantar American Academy of Project Management, inda daga nan ya wuce Israila don fadada karatun shi a Jami'ar Cornerstone, bayan ya kammala, bai tsaya nan ba ya halarci cibiyar International Security Organization Kilgore, wacce take da hadin gwiwa da mashahuriyar makarantar nan ta Kasar Indiya wato School of Profiling and Graphology, sannan ya je Kasar Kenya inda ya yi karatu a Kwalejin Pan-African Shield Collage da ke kasar.
Matashin dan siyasar mai jini a jika, ya mallaki kwalayen karatu da kwasa-kwasai daban-daban, sannan kwararre ne a fannin siyasa da ilimin sha'anin tsaron kasa da sanin tattalin arziki.
Shi ne Shugaban Gidauniyar Almajirai Empowerment Foundation, gidauniyar da ta yi fice a fadin Nijeriya da kasashen ketare wajen tallafa wa almajirai da mabukata.
El-Dabi ya bada gagrumar gudunmuwa wajen kawar da gwamnatin Jonathan da dora ta Shugaba Buhari a 2015 da 2019.
Ya taba rike mukamin Sakatare na Kasa na mata da matasa masu yi wa Buhari yakin neman zabe a 2019. Kuma ya zama mamba na kungiyar magoya bayan yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na APC a zaben 2019.
Haka zalika ya rike Daraktan Gudanarwa na magoya bayan Buhari a 2019, wato BSO a taqaice.
Shi ne Kwadineta na kungiyar magoya bayan Buhari daga 2014 zuwa 2015. Sannan mamba a babban kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa da sa ido kan lamuran zave a 2014.
Ya kuma rike sakatare na kasa na Kungiyar Buhari Support Group Center (BSGC) 2014. Sannan mamba a kwamitin shirya babban taron Jam'iyyar CPC a 2013. Da dai sauran mukamai da dama a siyasa wadanda suka yaukaka kyakkyawar alalarsa da Shugaba Muhammadu Buhari.
Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi), yana da kwarewa da gogewa wajen sanin hanyoyin tsaro da aikata miyagun laifuka, tare da binciken kwa-kwaf a matsayin sa gogaggen Akanta kuma masanin tattalin arziki da sarrafa kudaden kasa da sanin hanyoyin bunkasa saka hannayen jari a duniya baki daya.
Da irin wannan tarin baiwa, kwakwalwa, fasaha da fikira, ya kamata duk wata gwamnati da ke son cigaba da fuskoki da bangarori da dama, to ta saka irin su El-Dabi a gaba don baje baiwar da Allah Ya yi musu.
Hakika El-Dabi shugaba ne kuma jagora nagari.
Comments
Post a Comment