fusatattun matasa a Nijar sun bata allon wata hanya da aka saka sunan Shugaba Buhari
Fusatattun matasa a Nijar sun bata allon wata hanya da aka saka sunan Shugaba Buhari
Wasu fusatattun matasa a Nijar da ba a san ko su waye ba sun bata allon wata hanya da aka saka sunan Shugaba Buhari don karrama shi.
Matasan dai sun yi rubutu ne a jikin allon da jan fenti suna cewa Shugaba Buhari bai cancanta ba, inda suka kira shi da 'Crimanalle' wato mai laifi da harshen Faransanci.
Kwanaki ne Shugaba Bazoum ya gayyaci Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kaddamar da wasu ayyuka a kasar, inda ya bude wata hanya da aka sanya mata sunan shugaban na Nijeriya, lamarin da ake ganin wata babbar karramawa ce da ake yi wa Shugaba Buhari a kasashe makofta.
Comments
Post a Comment