Ya zuba wa abokinsa maganin bera a fura ya sha ya mutu, ya saka gawar a rijiya a Katsina
Ya zuba wa abokinsa maganin bera a fura ya sha ya mutu, ya saka gawar a rijiya a Katsina
SP Gambo Isa tare da wanda ake tuhuma
Daga Wakilinmu a Katsina
Wani mutum mai suna Laminu Saminu a qaramar hukumar Mani dake Jihar Katsina ya hallaka abokinsa Sanusi Bawa wanda jami'in tsaro ne mai muqamin mataimakin Sufritanda a hukumar tsaron farin kaya wato 'Civil Defense' reshen Jihar Katsina.
Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar SP Gambo Isa ne ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Talatar da ta gabata.
SP Isa ya bayyana cewar Saminu abokin marigayin ne domin kuwa ajinsu xaya a Kwalejin Horon Malamai dake Katsina, inda suke vangaren karatun digiri shekarar qarshe.
"Marigayin ya je gidan Saminu don ya duba lafiyarsa kasancewar ya kira wayar shi amma bai same shi ba.
"Ashe shi kuma tuni ya fara saqe-saqen yadda zai hallaka abokin nasa don ya sace motarsa da ya zo da ita gidan," inji SP Gambo Isa
SP Isa ya cigaba da cewa, "bayan marigayin ya ajiye motarsa launin kore mai lamba AA 266 KUF sai Saminu ya fita don ya sayo wa marigayin abinci.
"Kasancewar bai samu abincin ba sai ya sayo masa fura da nono. Daga nan sai ya zuba maganin vera cikin fura ya kuma ba shi ya sha, sai ya fita daga gidan bayan ya dawo ya tarar da marigayin ya galabaita amma bai mutu ba, sai ya xauko faskaren ita ce ya rinqa buga masa a kai har sai da ya tabbatar ya kashe shi, sannan ya xauki gawar ya jefa cikin rijiyar dake gidan.
"Daga nan sai ya xebo qasa da haki ya rufe marigayin a rijiyar," inji SP Isa.
Kakakin rundunar ya cigaba da cewa daga nan sai Saminu ya cire lambar motar marigayin.
Asirin shi ya tonu ne bayan da ya kira xaya daga cikin matan marigayin a waya inda ya yi mata qaryar cewar Kwastam sun qwace motar mijinta don haka ta ba shi takardun motar don ya je ya karvo.
Daga nan sai matar marigayin ta kai qara a ofishin Civil Defense inda maigidan nata ke aiki da kuma rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina.
SP Isa ya bayyana cewar binciken su ya nuna cewar shine ya aikata laifin bayan da ya kai 'yan sanda rijiyar da ya jefa marigayin.
Tuni dai aka tono gawar inda aka kai ta babbar asibitin Jihar Katsina don cigaba da gudanar da bincike.
Da aka tambayi wanda ake zargin yadda ya kashe abokin nasa sai ya ce, “Sunusi ya zo gidana ne don ya duba ni ya ga ko ina lafiya tunda ya kirawo wayata har kusan sau 11 amma ban xaga ba, to da ya zo ne bayan mun gaisa ya ce min ina ta kiran wayarka ba ka xauka ba, sai na ce mashi ban gani ba da ya ke na sanya ta caji ne, daga nan sai na ce mashi ya zo mu je wani gida da na kama ma wani abokina haya, to da muka je sai na buxe ma shi gareji ya sanya motar shi saboda ba ya son yara su gogar mashi mota.
"Bayan mun shiga gidan sai na fito don in samo mashi abinci, da na je ban samu abincin ba sai na sanya aka dama ma shi fura daga nan ne wata zuciya ta raya min in sanya mashi maganin vera a ciki shine na saya na sanya na ba shi ya sha,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, ”bayan ya sha furar da maganin veran ne sai ya fara galabaita, ni kuma sai na xauko wani icce na buga mashi a kai da ya mutu na sanya gawar rijiya.”
Daga qarshe kakakin rundunar 'yan sandan ya yi kira ga al'umma da su san irin mutanen da suke abota da su.
Comments
Post a Comment