Yadda 'yan bindiga suka bude wuta a masallaci a Katsina
Yadda 'yan bindiga suka bude wuta a masallaci a Katsina
Daga Wakilinmu
Mahara ɗauke da muggan bindigogi sun dira garin Maigamji da ke Ƙaramar Hukumar Funtua, inda su ka buɗe wa masallata wuta, lokacin da su ke Sallar Isha’i.
Mummunan al’amarin ya faru ranar Asabar da dare, inda bayan sun ji wa wasu da dama raunuka, su ka yi awon-gaba da mutum 19.
Wani da ya arce da kyar mai suna Bashir Murtala, ya shaida wa wakilin mu cewa ya na sahu na uku a cikin masallacin, yayin da aka fara buɗe masu wuta.
“Ana tsakiyar Sallah sai ji mu ka yi su na cewa kowa ya fita ya bi su. Maimakon a bi su, duk kowa sai ya kama gudun kuɓuta. A wannan gudun ne har aka raunata Liman Malam Yusha’u da kuma wasu da dama.
“Sun tafi da mutum 19, amma daga baya ‘yan bijilante da ke ƙauyen sun bi su har su ka ceto mutum shida, yanzu saura 13 kenan a hannun su,” Cewar Bashir.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Katsina Gambo Isa, ya tabbatar da kai farmakin, amma kuma ya ce da taimakon ‘yan sanda aka ceto mutanen shida.
Daidai lokacin da ‘yan bindiga ke Maigamji, wasu maharan sun kutsa garin Sayaya cikin Ƙaramar Hukumar Matazu, inda su ka kashe wani tsohon Daraktan Shiyya na Hukumar NABTEB, mai suna Hamisu Mamuda, kuma su ka arce da mutane da dama.
Kafin kisan na sa, wanda wasu da dama su ke cunne aka yi masa, Hamisu Mamuda shi ne Galadiman Ayyukan Matazu.
Comments
Post a Comment